Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya bayyana jami’an gwamnati da ake zargi da hannu a badakalar Presidential Foreign Investment Promotion Council (PFIPC).
Atiku ya ce rahoton wucin gadi na ICPC bai wanke fadar shugaban ƙasa ba, domin ya nuna akwai sakaci da kuma yiwuwar haɗin gwiwa a cikin tsarin gwamnati. Ya tambayi yadda wani da ake zargi da kasancewa ɗan damfara ya samu damar shiga ofisoshin gwamnati da amfani da takardun gwamnati.
Ya ce rahoton ya ƙara nuna cewa lamarin ba aikin mutum guda ne kawai ba, yana mai neman a bayyana waɗanda suka ba da damar ƙirƙirar hukumar bogi, amfani da takardar naɗin bogi da kuma buɗe asusun banki da sunan hukumomin ƙarya. Atiku ya kuma nemi a gudanar da bincike mai zaman kansa kan lamarin.
Atiku ya bukaci Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta gudanar da zaman sauraron jama’a kan badakalar, tare da watsa shi kai tsaye. Ya ce hakan zai bai wa waɗanda ake zargi damar bayar da shaida a bainar jama’a, yana mai cewa duk wani abu da bai kai ga buɗaɗɗen bincike ba zai ƙara jefa mutane cikin shakku kan ko ana kare wasu masu hannu a lamarin.

