Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana alkawarin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, na dawo da tallafin man fetur idan ya ci zaɓen 2027 a matsayin “yaudara”, yana mai cewa hakan ba zai yiwu ba kuma zai cutar da tattalin arzikin Najeriya.
Sani ya ce Najeriya ba za ta iya komawa tsarin tallafin man fetur da ya ce a baya ya janyo kashe tiriliyan naira tare da ƙara cin hanci da fasa-ƙwaurin man fetur ba. Ya ce kamata ya yi shugabanni su mayar da hankali wajen farfaɗo da matatun mai na ƙasar.
Ya bayyana cewa Najeriya ta kashe tsakanin Naira tiriliyan 3 zuwa 4 wajen tallafa wa kayayyakin man fetur, yana mai cewa hakan ba shi da ɗorewa ga ƙasar da ke samar da ɗanyen mai. Ya kuma zargi wasu mutane da karkatar da kuɗaɗen gwamnati a ƙarƙashin sunan shigo da man fetur.
Shehu Sani ya amince cewa cire tallafin man fetur ya jefa ’yan Najeriya cikin tsananin wahala, amma ya ce mafita ba ita ce komawa tsohon tsarin ba. Ya ƙara da cewa dawo da tallafin ba zai rage farashin kayayyaki ba, sai dai ya dagula daidaiton tattalin arzikin ƙasar.
Tsohon sanatan ya kuma yi kira da a ƙara zuba jari wajen tace mai a cikin gida, tare da kawo matatar Dangote a matsayin misali. A kan zaɓen 2027 kuwa, ya yi kira ga ’yan siyasa su yi kamfen bisa manufofi da shirye-shirye, tare da fifita haɗin kan Najeriya a kan bambancin ƙabila da addini.

