Jami’an tsaro a birnin Bengaluru na ƙasar Indiya sun kama wani ɗan Najeriya mai suna Samuel Ikkena bisa zargin jagorantar babbar hanyar safarar miyagun ƙwayoyi, inda aka kwato kwayar MDMA mai darajar sama da Naira miliyan 290. An ce kamen na cikin wani samame da ake yi domin dakile yaduwar miyagun ƙwayoyi a birnin.
Rahotanni sun bayyana cewa Ikkena, mai shekaru 44, ya shigo Indiya tun 2012 da bizar kasuwanci, inda ya fara sana’ar sayar da tufafi kafin ya koma Bengaluru a 2025. Ana zargin ya dade yana harkar safarar ƙwayoyi amma ya fake kasuwancin tufafi, yana saye tare da sayarwa ta hanyar wata ƙungiya da ya kafa.
Jami’an ‘yan sanda sun ce sun kwato kilogram 2 na MDMA da wasu nau’ikan ƙwayoyi kamar cannabis da heroin, tare da kama mutane 11 a wannan samame. Sun kuma bayyana cewa suna ci gaba da bincike domin gano manyan jagororin da ke bayan wannan haramtacciyar harkar.

