Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Edo, Blessing Agbebaku, ya yi murabus daga mukaminsa a ranar Litinin, yayin da wasu ’yan majalisar ke shirin tsige shi.
Mataimakiyar yada labaransa, Ivy Adodo-Ebojele, ce ta tabbatar da murabus din a wani sako da ta wallafa a Facebook. Ta ce za a bayyana karin bayani kan dalilan da suka sa kakakin ya sauka daga mukamin daga baya.
Murabus din Agbebaku ya jefa Majalisar Dokokin Jihar Edo cikin sabon rikicin shugabanci, yayin da ake sa ran ’yan majalisar za su dauki matakin zabar sabon kakaki.
Ivy ta tabbatar da murabus din ne ta hanyar rubuta cewa: “EDO ASSEMBLY SPEAKER RT HON CHIEF BLESSING AGBEBAKU RESIGNS.” Sai dai har yanzu ba a bayyana karin bayanai kan cikakken yanayin murabus din ba.

