Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ɗage yanke hukunci kan ƙarar da Hukumar EFCC ta shigar domin neman a ƙwace kadarori 57 da ake zargin suna da alaƙa da tsohon Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Tarayya, Abubakar Malami (SAN). Kotun ta sanya 10 ga Yuli, 2026 a matsayin ranar yanke hukunci.
EFCC ta buƙaci kotun ta tabbatar da ƙwace kadarorin har abada, tana mai cewa bincikenta ya nuna an mallake su ne da kuɗaɗen da ake zargin an samo ta haramtacciyar hanya. Sai dai Malami ya musanta zargin, yana cewa kadarorin nasa an same su ta halal, kuma EFCC ba ta gabatar da hujjojin da ke haɗa su da wani laifi ba.
Ana sa ran hukuncin zai fayyace ko kotun za ta amince da buƙatar EFCC ko kuma ta yi watsi da ita. Ana kallon shari’ar a matsayin ɗaya daga cikin manyan shari’un kwace kadarori da EFCC ke gudanarwa kan tsoffin jami’an gwamnati.

