Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanar da tsawaita wa’adin ci gaba da rajistar masu zaɓe na tsawon makonni biyu domin bai wa ‘yan Najeriya da suka cancanta ƙarin damar yin rajista. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Hukumar, Mohammed Kudu Haruna, ya sanya wa hannu.
Hukumar ta ce ta ɗauki matakin ne bayan nazarin yadda aikin rajistar ke gudana da kuma la’akari da shawarwarin da ta samu daga ofisoshinta na jihohi, jam’iyyun siyasa, ƙungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki. A cewarta, aikin da ya fara 18 ga Agustan 2025 kuma aka tsara ya ƙare 10 ga Yulin 2026, yanzu zai ci gaba har zuwa Lahadi 26 ga Yulin 2026.
INEC ta kuma sanar da ƙaddamar da tsarin rajistar kai tsaye ta intanet ga masu yin rajista karo na farko, wanda zai fara aiki daga 8 ga Yulin 2026. BechiHausa ta ruwaito cewa masu son yin rajista za su iya amfani da shafin intanet na hukumar domin kammala rajistarsu.

