Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta sun daƙile wani yunƙurin satar mutane a ƙauyen Jotar da ke kusa da shingen binciken ababen hawa na Quarantine a Jihar Benu. Hakan ya faru ne bayan samun sahihan bayanan sirri a ranar 2 ga Yulin 2026, wanda ya sa jami’an tsaro suka yi gaggawar kai ɗauki.
Sanarwar rundunar ta ce da isar dakarunta wurin, sun yi artabu da maharan bayan sun buɗe musu wuta, lamarin da ya haifar da musayar harsasai. A yayin arangamar, an kashe mutum guda da ake zargin ɗan ta’adda ne tare da ƙwato bindiga ƙirar AK-47 da kwanson harsasai guda biyu.
Rundunar ta bayyana cewa akwai alamun wanda aka kashe na iya kasancewa cikin gungun masu laifi da suka kai hari kan matafiya a ranar 1 ga Yulin 2026.

