Majalisar Shurar Ɗariƙar Tijjaniyya ta bayyana goyon bayanta ga sake zaɓen Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a wa’adi na biyu. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Darakta Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gidan Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Juma’a, 3 ga Yulin 2026.
Shugaban Majalisar Shurar Tijjaniyya, Sheikh Sani Shehu Maihula, ya bayyana hakan ne yayin taron Zikr da addu’ar ƙasa da ɗariƙar ta shirya a Fadar Mai Martaba Sarkin Kano, ta bakin ɗan’uwansa kuma mai magana da yawun majalisar, Sheikh Ibrahim Shehi Maihula (Shehi Shehi). Ya ce majalisar ta cimma matsaya ɗaya wajen marawa gwamnan baya saboda salon mulkinsa, bunƙasa darajojin Musulunci da manufofin da suka shafi al’umma.
Da yake mayar da martani, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gode wa shugabanni da mambobin Majalisar Shurar Tijjaniyya bisa addu’o’i da amincewar da suka nuna masa. Gwamnan ya sake jaddada aniyarsa ta ci gaba da gudanar da mulki cikin adalci da riƙon amana, tare da gode wa malaman addini kan rawar da suke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Jihar Kano.

