Shugaban Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Zamfara, Dr. Jamil Jibo Magayaki, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) bayan sauya sheƙar da gwamnan jihar Dauda Lawal ya yi zuwa jam’iyyar mai mulki.
Magayaki ya sanar da matakin nasa ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, inda ya ce ya yanke shawarar shiga APC ne bisa la’akari da halin siyasar da ake ciki a jihar Zamfara a halin yanzu.
Ya bayyana cewa sauya sheƙar tasa ta samo asali ne daga bukatar haɗa kai da wata jam’iyya da ta fi dacewa wajen tunkarar matsalolin tsaro, ci gaba da kuma kyakkyawan shugabanci domin amfanin al’ummar jihar.

