Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce al’ummar Hausawa na daga cikin ginshiƙan da ke taka muhimmiyar rawa wajen haɗin kai da ci gaban Najeriya.
Ya ce harshen Hausa ya bunƙasa sosai, kuma ya zama wani babban harshe na haɗin kai da kasuwanci a sassa daban-daban na duniya.
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake taya ɗimbin al’ummar Hausawa murnar Ranar Hausa, wadda ake gudanarwa a yau Laraba a fadar masarautar Daura mai tarihi.
Shugaban ya taya al’ummar Hausawa murna bisa wannan rana, tare da bayyana bikin da ake gudanarwa a Daura a matsayin wani muhimmin abu ga al’ummar Hausawa.

