Jami’an tsaro sun ceto mutum tara da aka yi garkuwa da su a Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna bayan sun fafata da ’yan bindiga, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa su bar waɗanda suka sace. Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta bayyana cewa an sace mutanen ne daga gonakinsu a ranar Laraba.
Rundunar ta ce bayan samun sahihan bayanan sirri, jami’an tsaro sun kai samame inda suka yi artabu da ’yan bindiga. Bayan ceto mutanen da aka sace tare da haɗa su da iyalansu, maharan sun yi wa jami’an tsaron kwanton ɓauna yayin da suke dawowa daga aikin.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, Rabiu Muhammad, ya jajanta wa iyalan jami’an biyu da suka rasu, yana mai yabawa jarumtakar su da sadaukarwar da suka yi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma. BechiHausa ta ruwaito cewa rundunar ta ce bincike na ci gaba domin kamo maharan tare da gurfanar da su a gaban doka.

